WAƘAR KYAUN ALƘAWARI
Ina maka sallama Ya Baba Buhari miji ga Indo Na zo ni da lalama Amsa mini, kar da ka sa ni kwando Tuni na taho na ma Ƙafa ɗaya kar mu saka a wando Waɗanda ka kai sama Babanmu, suna maka Babarodo Wa aufu bil Ahad Haka Rabbi Ya ce, maza je ka duba A kundi ka tarad- Da faɗinSa Ilahi ba ka musa ba Hakan kuma in Arad- Ta, sani nasa ba wahala yake ba Ina yi ma tuni Duka alƙawarinka da kai ka ɗauka Ka kwana cikin sani Lallai ka cika kafin ka sauka Abinci da magani Fa suna nema su fi kan talakka Shin Baba kana gani? Fa farashin fetur ya ƙi sauka Ka tuno da batun tsaro, Da ka ce ba shakka za shi samu? Tashar ruwa can Baro Ka ce mana zaka yi kar mu damu Lantarki tasgaro Nasa, ka ce zaka cire shi kanmu Ka ce mana aiyuka Ga matasa kowa za shi sāma Birni har ƙauyuka Hanyoyi ka ce, mun tuna ma Darajar Naira haka Ka ce sai ta kamo Dala ma Da rifainare duka Gyaransu ina daɗa dai tuna ma Harkar noma Da kai ta faɗi, yau Baba ina ta dosa? Ilimi, ƙasa har sama Shin wai harkar ga ina ta nausa? Ƙasar nan ta...