Posts

WAƘAR KYAUN ALƘAWARI

Image
Ina maka sallama Ya Baba Buhari miji ga Indo Na zo ni da lalama Amsa mini, kar da ka sa ni kwando Tuni na taho na ma Ƙafa ɗaya kar mu saka a wando Waɗanda ka kai sama Babanmu, suna maka Babarodo Wa aufu bil Ahad Haka Rabbi Ya ce, maza je ka duba A kundi ka tarad- Da faɗinSa Ilahi ba ka musa ba Hakan kuma in Arad- Ta, sani nasa ba wahala yake ba Ina yi ma tuni Duka alƙawarinka da kai ka ɗauka Ka kwana cikin sani Lallai ka cika kafin ka sauka Abinci da magani Fa suna nema su fi kan talakka Shin Baba kana gani? Fa farashin fetur ya ƙi sauka Ka tuno da batun tsaro, Da ka ce ba shakka za shi samu? Tashar ruwa can Baro Ka ce mana zaka yi kar mu damu Lantarki tasgaro Nasa, ka ce zaka cire shi kanmu Ka ce mana aiyuka Ga matasa kowa za shi sāma Birni har ƙauyuka Hanyoyi ka ce, mun tuna ma Darajar Naira haka Ka ce sai ta kamo Dala ma Da rifainare duka Gyaransu ina daɗa dai tuna ma Harkar noma Da kai ta faɗi, yau Baba ina ta dosa? Ilimi, ƙasa har sama Shin wai harkar ga ina ta nausa? Ƙasar nan ta...

WAƘAR YABON HARSHEN HAUSA

Image
Hausar ga dai harshenmu ne    Harshenmu ko siffarmu ne        Adabinsa hoton kanmu ne              Dube mu ko baka gan mu ba Allah gwani sarkin isa    Ka nufe ni in je Na'isa          Ƙofar gari na ci karfasa               Hausar uwata in yaba Harshe na Hausa matso ka ji    Yaren da shi ne yag gaji-          Da waɗanda yau suka fara ji               Shi ba dabo ne yin sa ba In kai nufin zance da shi    Ka tsaya ka karkaɗe dasashi           Zaƙi gare shi ya daƙƙashi                Ba zaka so baka ji shi ba Ita Hausa yaka taho jaɓe     Nau'i tili ne rakaɓe-           A cikinta, ba wani shaguɓe                 Ba zaka gane dukanta ba A gabas...