WAƘAR YABON HARSHEN HAUSA
Hausar ga dai harshenmu ne
Harshenmu ko siffarmu ne
Adabinsa hoton kanmu ne
Dube mu ko baka gan mu ba
Allah gwani sarkin isa
Ka nufe ni in je Na'isa
Ƙofar gari na ci karfasa
Hausar uwata in yaba
Harshe na Hausa matso ka ji
Yaren da shi ne yag gaji-
Da waɗanda yau suka fara ji
Shi ba dabo ne yin sa ba
In kai nufin zance da shi
Ka tsaya ka karkaɗe dasashi
Zaƙi gare shi ya daƙƙashi
Ba zaka so baka ji shi ba
Ita Hausa yaka taho jaɓe
Nau'i tili ne rakaɓe-
A cikinta, ba wani shaguɓe
Ba zaka gane dukanta ba
A gabas Kananci ne haye
Sai kattsinanci kewaye
Hausar Gumal ka ji na tsaye
Ba wacce ba zan ji ta ba
Hausar Katagum ce gaba
Ta Hadeja can ma jarraba
Su ne gabas ko dan gaba
Ban san akwai madadinsu ba
Can yamma ka ga akwai Aranci
Sakkwatanci kwai azanci
Kurfayanci, Zamfaranci
Ban gamo zanensu ba
Haka nan karin harshen Kabawa
Nan gusun ko da Adarawa
Na tuno Daurar Dumawa
Ba ko zan ƙi faɗarta ba
Zo nan mu je ka ji ɗan'uwa
Ban so ka je ka yi makkuwa
Harshenmu bai son ruɗuwa
Mai yi ba zai koye shi ba
Taso mu je, ta so mu tai
Nijje, na je, nittai na kai
Na ije, na ajje na aje, wai
Watta ba Hausarmu ba?
Gintce da gintse, ja haɗe
Hulla da hula, karkaɗe
Da Ƙahwa ƙafarka naɗe haɗe
Hausarmu ba kurar mu ba
Su ɗuwawuka da ɗuwaiwaka
Da ɗuwainiya da masarɓaka
Ma'anarsu ɗai haka yaz zaka
Ba mai musu ba mu haushi ba
Kwana shi kai, bacci yake
Ya tashi, hwalke idon shi ke
Zai zo shi, zakkowa shi ke
Ɗan gwari ba zai ji ki ba
Tamri da tauri namu ne
Arme a ɗarma waninmu ne
Dan gobe auren ɗanmu ne
Ban san akwai tamkarmu ba
Da wa"in da wannan in ka ji
Ma'anarsu ɗai a wurin gwaji
Bari daina neman agaji
Ɗauko guda ka iza gaba
Salga, masai shadda duka
Sayyi fitsari ma haka
Ɗan ɓulguce, guntu saka
Ma'anarsu ɗai mu wuce gaba
A Kano mu ce mata gujjiya
Ƙwaruru gun wasu ka jiya
Taɓanni ce dalbejiya
Waye ba zai ilmanta ba?
Kai ni bara na tsaya haka
Yarenmu ai ya haɓɓaka
Har Hindu har su ƙasar Makka
Ba inda ma ba a san shi ba
Mamman Nasar ɗan Ahmadu
Nai alƙawar kuma ba gudu
Zan ɗauki Hausa na kai Kudu
Yarensu bai kai namu ba
Tammata bi hamdika mai duka
Nasir ya tsaro baituka
Dan waƙe Hausa a harsuka
Yaren da ban ga kamarsa ba
©Nasir Ahmad Sadiq

Comments
Post a Comment