WAƘAR KYAUN ALƘAWARI
Ina maka sallama
Ya Baba Buhari miji ga Indo
Na zo ni da lalama
Amsa mini, kar da ka sa ni kwando
Tuni na taho na ma
Ƙafa ɗaya kar mu saka a wando
Waɗanda ka kai sama
Babanmu, suna maka Babarodo
Wa aufu bil Ahad
Haka Rabbi Ya ce, maza je ka duba
A kundi ka tarad-
Da faɗinSa Ilahi ba ka musa ba
Hakan kuma in Arad-
Ta, sani nasa ba wahala yake ba
Ina yi ma tuni
Duka alƙawarinka da kai ka ɗauka
Ka kwana cikin sani
Lallai ka cika kafin ka sauka
Abinci da magani
Fa suna nema su fi kan talakka
Shin Baba kana gani?
Fa farashin fetur ya ƙi sauka
Ka tuno da batun tsaro,
Da ka ce ba shakka za shi samu?
Tashar ruwa can Baro
Ka ce mana zaka yi kar mu damu
Lantarki tasgaro
Nasa, ka ce zaka cire shi kanmu
Ka ce mana aiyuka
Ga matasa kowa za shi sāma
Birni har ƙauyuka
Hanyoyi ka ce, mun tuna ma
Darajar Naira haka
Ka ce sai ta kamo Dala ma
Da rifainare duka
Gyaransu ina daɗa dai tuna ma
Harkar noma
Da kai ta faɗi, yau Baba ina ta dosa?
Ilimi, ƙasa har sama
Shin wai harkar ga ina ta nausa?
Ƙasar nan tai kama
Da a ce fim ne da ake da wasa
Rashawa, ta'adin kuɗi
Ka ce ba mai kuma yin sa, Baba
Kai ne fa kake faɗi
Ka ja layi ko baka faɗi ba?
Ka sha yin gargaɗi
Sai dai ba ka ɗau hanyar hani ba
To ko dai sai baɗi,
Sannan za kai aikinka Baba?
Har ka fi rabi
Cikin shekarun mulkinka; kana tunawa?
Ka yi wa Allah ka bi
Duk alƙawarinka ka zam cikawa
Ka daure ka yi zubi
Don ko su Wa'e basa iyawa
Ni dai ga shawara
Na baka ka zam ɗaukarta yanzu
Ha'inci, damfara
Su ke hana duk mulki ya wanzu
Ka yi nesa da yaudara
Ita ce ta kashe wancan na dazu
A kul ka bi gambara
Mai saurarenta yana awazzu
Naso ke ma tuni
Don so da ganin girma da ƙauna
Allah ma Ya sani
Talakawa duk sun yanke ƙauna
Mun yi maka lamuni
Kuma zamu taya ka ka yaƙi 'barna
©Nasir Ahmad Sadiq
(Mamman Naso)

Comments
Post a Comment